806 B
806 B
Maikayel
Gaskiya
Maikayel shi ne sarki cikin dukkan tsarkakan Allah, mala'ikun dake masa biyayya. Shi ne kaɗai mala'ikan da aka ambata musamman "babban mala'ika na Allah.
- Wannan kalma "babban mala'ika" na nufin "mafi girma cikin mala'iku" ko "mala'ika mai mulki."
- Makel mayaƙi ne dake yaƙar maƙiyan Allah yana kare mutanen Allah.
- Ya bida Isra'ilawa yaƙi gãba da rundunar Fasiya. A ƙarshen zamani zai bida rundunonin Isra'ila a yaƙi na ƙarshe gãba da ikokin mugunta, kamar yadda Daniyel ya yi anabci.
- Akwai mazaje da dama a Littafi Mai Tsarki masu suna Makel. Mazaje da yawa an ambacesu da sunan "ɗan Maikayel."
(Hakanen duba: mai'laka, Daniyel, manzo, Fasiya)
Wurarea da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Daniyel 10:13
- Daniyel 10:21
- Ezra 08:08
- Wahayin Yahaya 12:7-9