831 B
831 B
teku, Babban Teku, Tekun yamma, Baharmaliya
Gaskiya
A cikin Littafi Mai Tsarki, "Babban Teku" ko "tekun yamma" ana nufin ruwan nan da ake kira "Baharmaliya," shi ne babban ruwan da mutanen lokacin Littafi Mai Tsarki suka sani.
- Baharmaliya tana iyaka da Isra'ila (gabas), Turai (arewa da yamma), da Afrika (kudu)
- Wannan teku yana da mahimmanci a zamanin dã domin kasuwanci da tafiya saboda yana da gacin da ya shafi ƙasashe da yawa. Birane da kabilunda suke zaune a gaɓarsa sun azurta ƙwarai domin kwashe kaya daga wata ƙasa yafi sauƙi da jirgin ruwa.
- Tunda Babban Teku yana yamma da Isra'ila, saboda haka ne ake ce da shi "Tekun yamma."
(Hakanan duba: Isra'ila, kabilu, azurta)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ezekiyel 47:5-17
- Ezekiyel 47:18-20
- Yoshuwa 15:3-4
- Littafin Lissafi 13:27-29