1.1 KiB
1.1 KiB
Manasse
Gaskiya
Akwai mutane biyar da ake kiransu da sunan Manasse a cikin Tsohon Alƙawari:
- Manasse sunan ɗan farin Yosef ne.
- Manasse da ƙanensa Ifraim Yakubu mahaifin Yosef ya karbe su tankar 'ya'yansa wannan ya ba zuriyarsu 'yancin zama cikin kabilu goma sha biyu na Isra'ila.
- Zuriyar Manasse ta zama ɗaya daga cikin kabilun Isra'ila.
- Yawancin lokaci ana kiran kabilar Manasse "rabin kabilar Manasse" domin wani sashen kabilar ne suka zauna a cikin ƙasar Kan'ana yamma da Kogin Yodan. Sauran kabilar suka zauna a gabashin Yodan.
- Guda daga cikin sarakunan Yahuda shi ma ana kiransa Manasse.
- Sarki Manasse mugun sarki ne wanda ya bada 'ya'yansa hadayar ƙonawa ga gumaku.
- Allah ya hukunta Sarki Manasse ya bari abokan gãba suka cafke shi. Daga baya Manasse ya juyo ya rushe bagadai inda ake sujada ga gumaku.
(Hakanan duba: bagadi, Dan, Ifraim, Ezra, gumaka, Yakubu, Yahuda, al'ummai, kabilu goma sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi mai Tsarki:
- 2 Tarihi 15:09
- Maimaitawar Shari'a 03:12-13
- Farawa 41:51
- Farawa 48:1-2
- Littafin Alƙalai 01:27-28