655 B
655 B
Malakai
Gaskiya
Malakai ɗaya ne daga cikin annabawan Allah zuwa ga mulkin Yahuda. Ya kasance misalin shekaru 500 kafin Almasihu ya zo duniya.
- Malakai yayi annabci a lokacin da ake gina haikalin Isra'ilawa bayan komowarsu daga bautar talala a Babila.
- Ezra da Nehemiya sun yi rayuwa a lokaci guda da Malakai.
- Littafin Malakai shi ne littafi na ƙarshe a Tsohon Alƙawari.
- Kamar dukkan annabawan Tsohon Alƙawari, Malakai ya matsa wa mutane su tuba daga zunubansu su juyo ga yin sujada ga Yahweh.
(Hakanan duba: Babila, kamamme, Ezra, Yahuda, Nehemiya, Annabi, tuba, juyowa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Malakai 01:01