870 B
870 B
Masidoniya
Gaskiya
A lokatan Sabon Alƙawari, Masidoniya wani lardin Roma ne wanda ke yamma da Giris ta zamanin dã.
- Wasu mahimman biranen Masidoniya da Littafi Mai Tsarki ya faɗa sune Bereya, Filifai da Tasalonika.
- Tawurin wahayi Allah ya ce wa Bulus ya yi wa'azin bishara a Masidoniya.
- Bulus da abokan aikinsa suka tafi Masidoniya suka koya wa mutanen can game da Yesu suka kuma taimaki sabobbin tuba su yi girma cikin bangaskiyarsu.
- A cikin Littafi Mai Tsarki akwai wasiƙu da Bulus ya rubuta wa masu bada gaskiya a biranen Masidoniya kamar su Filifai da Tasalonika.
(Hakanan duba: gaskatawa, Biriya, bangaskiya, labari mai daɗi, Giris, Filifai, Tasalonika)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tasalonikawa 01:6-7
- 1 Tasalonikawa 04:10
- 1 Timoti 01:01:3-4
- Ayyukan Manzanni 16:10
- Ayyukan Manzanni 20:1-3
- Filibiyawa 04:14-17