795 B
795 B
Luka
Gaskiya
Luka ya rubuta litattafai biyu na Sabon Alƙawari: bishara ta hannun Luka da Ayyukan Manzanni.
- A cikin wasiƙarsa ga Kolosiyawa, Bulus ya ambaci Luka likita ne. Bulus kuma ya yi faɗi a kan Luka a cikin wasu wasiƙunsa guda biyu.
- Ana tsammani Luka ɗan harshen Girik ne kuma Ba'al'umme ne wanda ya zo ga sanin Yesu. A cikin Bishararsa, Luka ya faɗi a wurare da dama cikin rubutunsa da suka shaida ƙaunar Yesu ga dukkan mutane, Yahudawa da Al'ummai.
- Luka ya tafi tare da Bulus a cikin tafiyar bishararsa sau biyu ya taimake shi cikin aikinsa.
- A wasu rubutun ikilisiya ta farko, aka ce an haifi Luka a Antiyok ta Asiriya.
(Duba kuma: Antiyok, Bulus, Asiriya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Timoti 04:11-12
- Kolosiyawa 04:12-14
- Filimon 01:24