665 B
665 B
Lot
Gaskiya
Lot ɗan ɗan'uwan Ibrahim ne.
- Shi ɗan Haran ne ɗan'uwan Ibrahim.
- Lot ya tafi tare da Ibrahim zuwa ƙasar Kan'ana ya zauna a cikin birnin Sodom.
- Lot shi ne kakan Mowabawa da Ammoniyawa.
- Da sarakai maƙiya suka kai wa Sodom Hari suka kuma kama Lot, Ibrahim ya zo da ɗaruruwan mutane ya ƙwato Lot ya kuma karɓo kadarorinsa.
- Mutane dake zaune a birnin Sodom mugaye ne, saboda haka Allah ya hallaka birnin. Amma da farko ya faɗa wa Lot da iyalinsa su bar birnin domin su kuɓuta.
(Hakanan duba: Ibrahim, Ammon, Haran, Mowab, Sodom)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Bitrus 02:08
- Farawa 11:27-28
- Farawa 12:4-5