778 B
778 B
Lebanon
Gaskiya
Lebanon wata yankin ƙasa ce mai kyaun duwatsu a gaɓar Tekun Baharmaliya, arewa da Isra'ila. A lokacin Littafi Mai Tsarki wannan yanki kurmi ne cunkus da rimayen itatuwa kamar su sida da sifures.
- Sarki Suleman ya aika ma'aikata Lebanon su saro itatuwan sida domin amfani da su a ginin haikalin Allah.
- Lebanon ta dã da mazaunanta mutanen Fonisiya ne, ƙwararru a gine-ginen jiragen ruwa da ake amfani da su wajen kasuwanci masu armashi.
- Birane Taya da Sidon suna cikin Lebanon. A waɗannan birane a cikin su ne aka fara amfani da rinin shunayya.
(Hakanan duba: sida, sifires, fir, Fonisiya)
Wuraren da ake samunsu a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 04:32-34
- 2 Tarihi 02:8-10
- Maimaitawar Shari'a 01:7-8
- Zabura 029:3-5
- Zakariya 10:8-10