661 B
661 B
Liya
Gaskiya
Liya na ɗaya daga cikin matan Yakubu. Ita ce mahaifiyar goma daga cikin 'ya'ya maza na Yakubu kuma zuriyarsu sune goma daga cikin kabilu sha biyu na Isra'ila.
- Mahaifin Liya shi ne Laban, wanda kuma shi ɗan'uwan Rebeka ne mahaifiyar Yakubu.
- Yakubu bai ƙaunaci Liya ba kamar yadda ya ƙaunaci ɗaya matar tasa, Rahila, amma Allah ya albarkaci Liya a yalwace ta wurin ba ta 'ya'ya da yawa.
- Ɗan Liya Yahuda shi ne kakan Sarki Dauda da Yesu.
(Hakanan duba: Yakubu, Yahuda, Laban, Rahila, Rebeka, kabilu sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Farawa 29:17
- Farawa 29:28
- Farawa 31:06
- Rut 04:11