716 B
716 B
La'azaru
Gaskiya
La'azaru da 'yan'uwansa Mata, Maryamu da Marta, abokan Yesu ne na musamman. Yawanci Yesu na zama tare da su a Betani.
- La'azaru dai anfi saninsa game da al'amarin yadda Yesu ya tada shi daga mutuwa bayan an bizne shi cikin kabari kwanaki da yawa.
- Shugabannin Yahudawa suka fusata da Yesu kuma suka yi kishin ganin cewa ya yi wannan al'ajibi, suka kuma nemi hanyar kashe Yesu da La'azaru gabaɗaya.
- Yesu kuma ya yi misali da wani matalaucin mabaraci da wani mutum mai arziki inda mabaracin an kira shi da suna "La'azaru."
(Hakanan duba: mabaraci, shugabannin Yahudawa, Marta, Maryamu, tadawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Yahaya 11:11
- Yahaya 12:1-3
- Luka 16:21