827 B
827 B
Kedar
Gaskiya
Kedar ɗan Ishma'ila ne na biyu. Shima birni ne mai muhimmanci, wanda ake kyautata zaton an bashi suna bisa ga sunan mutumin.
- Birnin Kedar yana sashen arewacin Arabiya kusa da kudancin kan iyakar Falestin. A cikin lokuttan Littafi Mai Tsarki, an san shi saboda ƙasaitarsa da kyaunsa.
- Zuriyar Kedar suka zama babbar ƙungiyar mutane da suma ake kiransu "Kedar."
- Furcin "rumfunan Kedar masu duhu" yana nufin rumfunan gashin baƙaƙen awaki da mutanen Kedar suke zama a ciki.
- Waɗannan mutane na Kedar masu kiwon tumaki ne da awaki. Suna kuma amfani da raƙuma wajen ɗaukar kaya.
- A Littafi Mai Tsarki, furcin "ɗaukakar Kedar" na nufin ƙasaitar wannan birni da mutanensa.
(Hakanan duba: Arabiya, akuya, Ishma'ila, hadaya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Waƙar Suleman 01:05