992 B
992 B
Kadesh, Kadesh-Barniya, Meriba Kadesh
Gaskiya
Sunayen Kadesh, Kadesh-Barniya, Meriba Kadesh dukkansu na magana game da wani birni mai muhimmanci a tarihin Isra'ila wanda ke a sashen kudancin Isra'ila, kusa da lardin Idom.
- Birnin Kadesh wani kurmi ne, wurin da akwai ruwa da ƙasa mai albarka a tsakiyar hamada mai suna Zin.
- Musa ya aiki 'yan leƙen asirin ƙasa sha biyu zuwa ƙasar Kan'ana daga Kadesh Barniya.
- Isra'ila kuma sunyi sansani a Kadesh a lokacin yawonsu cikin jeji.
- A Kadesh Barniya ne Miriyam ta mutu.
- A Meriba Kadesh ne Musa ya yi rashin biyayya da Allah ya kuma bugi dutsen domin ya samar wa Isra'ilawa ruwa, a maimakon yiwa dutsen magana kamar yadda Allah ya gaya masa.
- Sunan "Kadesh" ya fito ne daga wata kalmar Ibraniyawa mai ma'ana "tsarki" ko "keɓaɓɓe."
(Hakanan duba: hamada, Idom, tsarki)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ezekiyel 48:28
- Farawa 14:7-9
- Farawa 16:14
- Farawa 20:1-3
- Yoshuwa 10:40-41
- Littafin Lissafi 20:1