1.1 KiB
1.1 KiB
Yahudiya
Gaskiya
Kalmar "Yahudiya" na nufin sashen ƙasa a tsohuwar Isra'ila. Wasu lokutta ana amfani da kalmar da matsastsitar manufa wasu lokuttan kuma da manufa mai fãɗi.
- Wasu lokutta "Yahudiya" ana amfani da ita da manufa a matse a matsayin wani lardi dake a kudancin tsohuwar Isra'ila yamma da Mataccen Teku. Wasu fassarorin sun kira wannan lardi "Yahuda."
- Wasu lokuttan "Yahudiya" ana amfani da ita da manufa mai fãɗi a matsayin dukkan lardunan tsohuwar Isra'ila, duk da Galili, Samariya, Feriya, Idumiya da Yahudiya (Yahuda).
- Idan masu fassara suna so su fito da bambancin sosai, Yahudiya mai manufa da fãɗi za a iya fassarawa a matsayin "Ƙasar Yahudiya" tunda wannan ne fannin tsohuwar Isra'ila wadda kabilar Yahuda suka zaune tun asali.
(Hakanan duba: Galili, Idom, Yahuda, Yahuda, Samariya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tasalonikawa 02:14
- Ayyukan Manzanni 02:09
- Ayyukan Manzanni 09:32
- Ayyukan Manzanni 12:19
- Yahaya 03:22-23
- Luka 01:05
- Luka 04:44
- Luka 05:17
- Markus 10:1-4
- Matiyu 02:01
- Matiyu 02:05
- Matiyu 02:22-23
- Matiyu 03:1-3
- Matiyu 19:01