848 B
848 B
Yahuda
Gaskiya
Yahuda na ɗaya daga cikin manyan 'ya'ya maza na Yakubu. Mahaifiyarsa ita ce Liya. Ana kiran zuriyarsa "kabilar Yahuda."
- Yahuda ne ya cewa 'yan'uwansa su saida ƙanensu Yosef a matsayin bawa a maimakon barinsa ya mutu a cikin rami mai zurfi.
- Sarki Dauda da dukkan sarakunan da suka biyo bayansa zuriyar Yahuda ne. Yesu, ma, zuriyar Yahuda ne.
- Sa'ad da mulkin Suleman ya ƙare kuma ƙasar Isra'ila ta rabu, masarautar Yahuda ita ce masarautar kudu.
- A cikin Littafin Wahayin Yahaya na Sabon Alƙawari, an kira Yesu "Zaki na Yahuda."
- Kalmomin "Bayahude" ko "Yahudiya" sun zo daga sunan "Yahuda ne."
(Hakanan duba: Yakubu, Bayahude, Yahuda, Yahudiya, kabilun Isra'ila sha biyu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 02:1-2
- 1 Sarakuna 01:09
- Farawa 29:35
- Farawa 38:02
- Luka 03:33
- Rut 01:02