859 B
859 B
Yotam
Gaskiya
A cikin Tsohon Alƙawari, akwai mutane uku masu suna Yotam.
- Wani mutum mai suna Yotam shine ɗan autan Gidiyon. Yotam ya taimaka aka kayar da yayansa Abimelek, wanda ya kashe dukkan sauran 'yan'uwansa maza.
- Wani kuma mutumin mai suna Yotam sarki ne bisa Yahuda har tsawon shekaru sha shidda bayan mutuwar mahaifinsa Uzziya ko (Azariya).
- Kamar mahaifinsa, Sarki Yotam yayi biyayya da Allah kuma sarki ne nagari.
- Duk da haka, yadda bai kawar da wuraren bautar gumaka ba yasanya mutanen Yahuda daga bisani suka sake kaucewa daga Allah.
- Yotam kuma yana ɗaya daga cikin kakannin da aka lissafa a cikin tarihin asalin Yesu Almasihu a cikin littafin Matiyu.
(Hakanan duba: Abimelek, Ahaz, Gidiyon, Uzziya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Tarihi 26:21
- 2 Sarakuna 15:05
- Ishaya 01:1
- Littafin Alƙalai 09:5-6