909 B
909 B
Yosiya
Gaskiya
Yosiya sarki ne mai tsoron Allah da yayi mulki a bisa masarautar Yahuda na tsawon shekaru talatin da ɗaya. Ya bida mutanen Yahuda suka tuba suka yi biyayya da Yahweh.
- Bayan an kashe mahaifinsa Sarki Amon, Yosiya ya zama sarki bisa Yahuda yana ɗan shekara takwas.
- A cikin shekaru sha takwas na sarautarsa, Sarki Yosiya ya umarci Hilkiya babban firist ya sake gina haikalin Ubangiji. Yayinda wannan ke faruwa, sai aka samo litattafan shari'a.
- Sa'ad da aka karantawa Yosiya litattafan Shari'ar, yayi ɓacin rai game da yadda mutanensa suka yi rashin biyayya ga Allah. Ya bada umarni a rushe dukkan wuraren bautar gumaka kuma a kashe firistocin allolin ƙarya.
- Ya kuma umarci mutane su fãra yin shagalin bukin Ƙetarewa.
(Hakanan duba: allahn ƙarya, Yahuda, shari'a, Ƙetarewa, haikali)
- 1 Tarihi 03:13-14
- 2 Tarihi 33:24-25
- 2 Tarihi 34:03
- Irmiya 01:03
- Matiyu 01:11