ha_tw/bible/names/joshua.md

1.4 KiB

Yoshuwa

Gaskiya

Akwai mutane Isra'ilawa da yawa masu suna Yoshuwa a cikin Littafi Mai tsarki. Wanda aka fi sani shine Yoshuwa ɗan Nun mataimakin Musa wanda kuma daga bisani ya zama muhimmin shugaba na mutanen Allah.

  • Yoshuwa na ɗaya daga cikin 'yan leƙen asirin ƙasa da Musa ya aika su tafi binciken ƙasar Alƙawari.
  • Tare da Kaleb, Yoshuwa ya roƙi mutanen Isra'ilawa da suyi biyayya da umarnin Allah su shiga Ƙasar Alƙawari su kayar da Kan'aniyawa.
  • Shekaru da yawa daga bisani, bayan mutuwar Musa, Allah ya zaɓi Yoshuwa ya bida mutanen Isra'ila zuwa Ƙasar Alƙawari.
  • A yaƙi na farko kuma wanda aka fi sani gãba da Kan'aniyawa, Yoshuwa ya bida Isra'ilawa suka kayar da birnin Yeriko.
  • Littafin Yoshuwa a Tsohon Alƙawari ya faɗi yadda Yoshuwa ya bida Isra'ilawa suka ɗauki mallakar Ƙasar Alƙawari da yadda kuma ya ba kowacce kabilar Isra'ila fannin ƙasar domin su zauna.
  • An kuma ambaci Yoshuwa ɗan Yozadak a cikin litattafan Haggai da Zakariya; shi baban firist ne wanda ya taimaka aka sake gina ganuwoyin Urshalima.
  • Akwai kuma mutane da yawa masu suna Yoshuwa da aka ambata a cikin tarihohin asali da saura wurare a Littafi Mai Tsarki.

(Hakanan duba: Kan'ana, Haggai, Yeriko, Musa, Ƙasar Alƙawari, Zakariya (Tsohon Alƙawari))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 07:25-27
  • Maimaitawar Shari'a 03:21
  • Fitowa 17:10
  • Yoshuwa 01:03
  • Littafin Lissafi 27:19