967 B
967 B
Yosef (Sabon Alƙawari)
Gaskiya
Yosef mahaifi ne ga Yesu a duniya ya kuma yi renon sa a matsayin ɗansa. Mutum ne mai adalci wanda aikinsa kafinta ne.
- Yosef yayi tashen wata yarinya Bayahudiya mai suna Maryamu, yayin da suke tashen sai Allah ya zaɓe ta ta zama mahaifiyar Yesu Almasihu.
- Wani mala'ika ya faɗi wa Yosef cewa Ruhu Mai Tsarki da aikin al'ajibi yasa Maryamu ta sami ciki, kuma jaririn Maryamu Ɗan Allah ne.
- Bayan da aka haifi Yesu, sai wani mala'ika ya gargaɗi Yosef cewa ya ɗauki jaririn da Maryamu ya tafi Masar domin su gudu daga Herod.
- Yosef da iyalinsa daga bisani sun yi zama a birnin Nazaret na Galili, inda yayi ta samun abin biyan buƙatu ta wurin sana'arsa ta kafinta.
(Hakanan duba: Almasihu, Galili, Yesu, Nazaret, Ɗan Allah, Budurwa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Yahaya 01:43-45
- Luka 01:26-29
- Luka 02:4-5
- Luka 02:15-16
- Matiyu 01:18-19
- Matiyu 01:24-25
- Matiyu 02:19-21
- Matiyu 13:54-56