666 B
666 B
Yoffa
Gaskiya
A zamanin Littafi Mai Tsarki, birnin Yoffa muhimmi ne wajen kasuwancin gaɓar teku wanda ke dai-dai Tekun Meditareniyan, kudu da Sararin Sharon.
- Tsohon birnin Yoffa yanzu aka fi sani da suna birnin Yaffa, wanda yanzu yake fannin birnin Tel Abib.
- A Tsohon Alƙawari, Yoffa birni ne inda Yona ya shiga jirgi zuwa Tarshis.
- A Sabon Alƙawari, wata mata kirista mai suna Tabita ta mutu a Yoffa, Bitrus kuma ya dawo da ita da rai.
(Hakanan duba: Teku, Yerusalem, Sharon, Tarshish)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 09:37
- Ayyukan Manzanni 10:08
- Ayyukan Manzanni 11:4-6
- Ayyukan Manzanni 11:11
- Yona 01:03