824 B
824 B
Yona
Gaskiya
Yona annabin Ibraniyawa ne a Tsohon Alƙawari.
- Littafin Yona ya faɗi labarin abin da ya faru sa'ad da Allah ya aiki Yona yayi wa'azi ga mutanen Nineba.
- Yona ya ƙi tafiya Nineba a maimako ma ya shiga jirgi mai tafiya Tarshis.
- Allah ya sanya wata babbar guguwar hadari ta sha ƙarfin jirgin.
- Ya gaya wa mutanen dake tuƙin jirgin cewa yana gujewa daga Allah ne, sai ya bada shawarar a jefa shi cikin tekun. Sa'ad da suka yi haka sai guguwar hadarin ta tsaya.
- Babban kifi ya haɗiye Yona, kuma ya kasance can cikin kifi har ranaku da dare uku.
- Bayan haka, Yona ya tafi Nineba ya kuma yiwa mutanen wa'azi a can, sai suka juya daga zunubansu.
(Hakanan duba: rashin biyayya, Nineba, juyawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Yona 01:03
- Luka 11:30
- Matiyu 12:39
- Matiyu 16:04