885 B
885 B
Yahaya (mai Baftisma)
Gaskiya
Yahaya ɗa ne ga Zekariya da Elizabet. Tunda "Yahaya" suna ne da aka saba da shi, yawancin lokaci ana kiransa "Yahaya mai Baftisma" domin a bambanta shi da sauran mutanen da ake kira Yahaya, kamar Manzo Yahaya.
- Yahaya annabi ne wanda Allah ya aiko domin ya shirya mutane su gaskata kuma su bi Almasihu.
- Yahaya ya faɗi wa mutane su furta zunubansu, su kuma dena yin zunubi, domin su zama a shirya su karɓi Almasihu.
- Yahaya yayi wa mutane da yawa baftisma a matsayin alamar ladama domin zunubansu kuma suna juyawa daga gare su.
- Yahaya dai ana kiran sa "Yahaya mai Baftisma" saboda yayi wa mutane da yawa baftisma.
(Hakanan duba: baftisma, Zekariya (Sabon Alƙawari))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Yahaya 03:22-24
- Luka 01:11-13
- Luka 01:62-63
- Luka 03:7
- Luka 03:15-16
- Luka 07:27-28
- Matiyu 03:13
- Matiyu 11:14