865 B
865 B
Yahaya (manzo)
Gaskiya
Yahaya na ɗaya daga cikin manzannin Yesu sha biyu kuma ɗaya daga cikin abokan Yesu na kurkusa.
- Yahaya da ɗan'uwansa Yakubu 'ya'ya maza ne na wani mai sana'ar kamun kifi wato Su mai suna Zebedi.
- A cikin bisharar daya rubuta game da rayuwar Yesu, Yahaya ya ambaci kansa a matsayin "Almajirin da Yesu ke ƙauna." Wannan na nuna cewa Yahaya wani muhimmin aboki ne na kurkusa da Yesu.
- Manzo Yahaya ya rubuta litattafai biyar na Sabon Alƙawari: bishara ta Yahaya, wahayin Yesu Almasihu, da wasiƙu uku da aka rubuta wa sauran masubi.
- A Lura da cewa manzo Yahaya daban yake da Yahaya mai Baftisma.
(Hakanan duba: manzo, bayyanawa, Yakubu (ɗan Zebedi), Yahaya (mai Baftisma), Zebedi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Galatiyawa 02:9-10
- Yahaya 01:19-21
- Markus 03:17-19
- Matiyu 01:1-3
- Wahayin Yahaya 01:1-3