643 B
643 B
Yezebel
Gaskiya
Yezebel ita ce muguwar matar Sarki Ahab na Isra'ila.
- Yezebel ta zuga Ahab da sauran Isra'ila suyi bautar gumaka.
- Ta kuma kashe annabawan Allah da yawa.
- Yezebel ta sanya mutum marar laifi mai suna Nabot a kashe shi saboda Ahab ya sãce garkar inabin Nabot.
- A ƙarshe ita ma Yezebel aka kashe ta saboda dukkan miyagun abubuwan da ta aikata. Iliya yayi anabcin yadda zata mutu kuma haka ya faru dai-dai yadda ya furta.
(Hakanan duba: Ahab, Iliya, allan ƙarya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 16:31-33
- 1 Sarakuna 19:1-3
- 2 Sarakuna 09:07
- 2 Sarakuna 09:31
- Wahayin Yahaya 02:20