ha_tw/bible/names/jeroboam.md

1.4 KiB

Yerobowam

Gaskiya

Yerobowam ɗan Nebat shine sarki na farko na masarautar arewa ta Isra'ila wajen shekaru 900-910 kafin haihuwar Almasihu. Wani Yerobowam ɗin, ɗan Sarki Yehowash, yayi mulki bisa Isra'ila wajen shekaru 120 daga bisani.

  • Yahweh yaba Yerobowam ɗan Nebat anabci cewa zai zama sarki bayan Suleman kuma zai yi mulki bisa kabilu sha biyu na Isra'ila.
  • Sa'ad da Suleman ya mutu, kabilu goma na arewacin Isra'ila suka yi tawaye gãba da Rehobowam ɗan Suleman a maimako suka maida Yerobowam ya zama sarkinsu, suka bar Rehobowam a matsayin sarkin kabilu biyu kacal na kudu, Yahuda da Benyamin.
  • Yerobowam ya zama mugun sarki wanda ya bida mutanen Isra'ila suka kauce daga bautawa Yahweh a maimako kuma ya kafa masu gumakai domin suyi masu bauta. Dukkan sarakunan Isra'ila suka bi misalin Yerobowam kuma suka zama miyagu kamar yadda shima yake.
  • Wajen shekaru 120 daga bisani, wani sarki Yerobowam ɗin ya fara mulkin masarautar arewa ta Isra'ila. Wannan Yerobowam ɗa ne ga sarki Yehowash kuma ya zama mugu kamar dukkan sarakunan Isra'ila da suka kasance a baya.
  • Duk da muguntar Isra'ilawa, Allah yayi masu jinƙai ya taimaki wannan sarki Yerobowam ya ci ƙasa ya kuma kafa iyakoki domin lardinsu.

(Hakanan duba: allolin ƙarya, masarautar Isra'ila, Yahuda, Suleman)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 05:16-17
  • 1 Sarakuna 12:02
  • 2 Tarihi 09:29
  • 2 Sarakuna 03:1-3
  • Amos 01:01