985 B
985 B
Yehu
Gaskiya
Yehu suna ne na mutum biyu a Tsohon Alƙawari.
- Yehu ɗan Hanani annabi ne a lokacin mulkin Sarki Ahab na Isra'ila da Sarki Yehoshafat na Yahuda.
- Yehu ɗa (ko zuriyar) Yehoshafat hafsa ne a rundunar sojojin Isra'ila wanda kuma aka shafe ya zama sarki ta wurin umarnin annabi Elisha.
- Sarki Yehu ya kashe miyagun sarakuna biyu, Sarki Yoram na Isra'ila da Sarki Ahaziya na Yahuda.
- Sarki Yehu kuma ya kashe dukkan dangin sarki Ahab na dã ya kuma sa aka kashe muguwar sarauniya Yezebel.
- Sarki Yehu ya rusar da dukkan wuraren sujadar Ba'al dake cikin Samariya ya kuma kashe dukkan annabawan Ba'al.
- Sarki Yehu ya bautawa Allah na gaskiya shi kaɗai, Yahweh, kuma shine sarki bisa Isra'ila na tsawon shekaru ashirin da takwas.
(Hakanan duba: Ahab, Ahaziya, Ba'al, Elisha, Yehoshafat, Yehu, Yezebel, Yoram, Yahuda, Samariya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 04:35
- 1 Sarakuna 16:02
- 2 Tarihi 19:1-3
- 2 Sarakuna 10:09
- Hosiya 01:04