712 B
712 B
Yehoshafat
Gaskiya
Yehoshafat suna ne na a ƙalla mutane biyu a Tsohon Alƙawari.
- Wanda aka fi sani da wannan suna shine sarki Yehoshafat wanda shine na huɗu wurin mulki bisa masarautar Yahuda.
- Ya maido salama tsakanin Yahuda da Isra'ila ya kuma rushe bagadan allolin ƙarya.
- Wani Yehoshafat ɗin "marubuci ne" domin Dauda da Suleman. Aikinsa ya haɗa da rubuta takardu domin sarki ya sa hannu da rubuta tarihin muhimman al'amura da suka faru a masarautar.
(Hakanan duba: bagadi, Dauda, allan ƙarya, Isra'ila, Yahuda, firist, Suleman)
Wurarenda ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 03:10-12
- 1 Sarakuna 04:17
- 2 Tarihi 17:01
- 2 Sarakuna 01:17
- 2 Sama'ila 08:15-18
- Matiyu 01:7-8