954 B
954 B
Ishma'il, Ba'Ishma'ile, Ishma'ilawa
Gaskiya
Ishma'il ɗan Ibrahim ne da Hajara baiwa daga Masar. Akwai sauran Mutane a cikin Tsohon Alƙawari da ke da suna Ishma'il.
- Ma'anar sunan nan Ishma'il ita ce "Allah na ji."
- Allah ya yi alƙawarin yiwa Ishma'il ɗan Ibrahim albarka, amma ba shi ba ne ɗan da Allah ya yiwa Ibrahim alƙawari ba.
- Allah ya kare Hajara da Ishma'il lokacin da aka tura su daji.
- A lokacin da Ishma'il ke cikin dajin Faran, ya auri ɗiyar masarawa.
- Ishma'il ɗan Netaniya hafsan soja ne daga Yahuda wanda ya jagoranci ƙungiyar mutane su kashe gwabna wanda sarkin Babila, Nebukadnezza ya naɗa.
- Akwai waɗansu maza huɗu dake Ishma'il a cikin Tsohon Alƙawari.
(Hakanan duba: Ibrahim, Babila, yarjejeniya, jeji, Masar, Hajara, Ishaku, Nebukadnezza, Faran, Saratu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 01:28-31
- 2 Tarihi 23:01
- Farawa 16:12
- Farawa 25:9-11
- Farawa 25:16
- Farawa 37:25-26