923 B
923 B
Ishaya
Gaskiya
Ishaya annabin Allah ne da ya yi anabci a kwanakin mulkin sarakuna huɗu na Yahuda, wato Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya.
- Ya rayu ne a Yerusalem a lokacin da Asiriyawa ke kaiwa birnin hari a kwanakin mulkin Hezekiya.
- Littafin Ishaya a cikin Tsohon Alƙawari na ɗaya daga babban litattafan a cikin Littafi Mai Tsarki.
- Ishaya ya rubuta anabce-anabcen da waɗansun su suka cika tun yana raye.
- Ishaya an san shi musamman kan anabcinsa da ya yi game da Mesaya wanda ya cika shekaru 700 bayan anabcin a lokacin da Yesu ke raye a duniya.
- Yesu da almajiransa sun yanko aya daga anabcin Ishaya domin su koyar da mutane game da Mesaya.
(Hakanan duba: Ahaz, Asiriya, Kristi, Hezekiya, Yotam, Yahuda, annabi, Uzziya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Sarakuna 20:1-3
- Ayyukan Manzanni 28:26
- Ishaya 01:1
- Luka 03:4
- Markus 01:01
- Markus 07:06
- Matiyu 03:03
- Matiyu 04:14