803 B
803 B
Hosheya
Gaskiya
Hosheya sunan wani sarki ne na Isra'ila da kuma sunan mutane da yawa a cikin Tsohon Alƙawari.
- Hosheya ɗan Ala sarkin Isra'ila ne na tsawon shekaru tara a waɗansu kwanaki na sarauta Ahaz da Hezekiya, sarakunan Yahuda.
- Yoshuwa ɗan Nun da sunansa Hosheya ne. Musa ya canza sunan Hosheya zuwa Yoshuwa kafin a aike tare da mutane sha ɗaya su leƙi asirin ƙasar Kan'aniyawa.
- Bayan mutuwar musa, Yoshuwa ya jagoranci mutanen Isra'ila domin su mallaki ƙasa kan'ana.
- Akwai wani mutum na dabam mai suna Hosheya ɗan Azaziya ɗaya kuma daga cikin shugabannin Ifraimawa.
(Hakanan duba: Ahaz, Kan'ana, Ifraim, Hezekiya, Yoshuwa, Musa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1Tarihi 27:20
- 2 Sarakuna 15:30
- 2 Sarakuna 17:03
- 2 Sarakuna 18:01
- 2 Sarakuna 18:09