754 B
754 B
Hosiya
Gaskiya
Hosiya annabi ne na Isra'ila wanda ya rayu ya kuma yi anabci a wajejen shekaru 750 kafin zuwan Kristi.
- Hidimarsa ta kai shekaru masu yawa har zuwa mulkokin sarakuna da yawa, kamar su Yerobowam, Zakariya, Yotam, Ahaz, Hosheya, Uzziya, da Hezekiya.
- Allah ya ce da Hosiya ya auri karuwa mai suna Gomar ya kuma ci gaba da ƙaunar ta, duk da yake bata da aminci a gare shi.
- Wannan na nuna ƙaunar Allah ga mutanensa marasa aminci, wato Isra'ila
- Hosiya ya yi anabci gãba da mutanen Isra'ila sabo da zunubansu, yana rinjayo su su juyo daga bautar gumaka.
(Hakanan duba: Ahaz, Hezekiya, Hosheya, Yerobowam, Yotam, Uzziya, Zakariya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Hosiya 01:1-2
- Hosiya 01:3-5
- Hosiya 01:6-7