957 B
957 B
Bahitte, Hittiyawa
Gaskiya
Hittiyawa su ne zuriyar Ham ta wurin ɗansa Kan'ana. Sun zama babbar daula da ke a wurin da yau ake kira Turkiyya da kuma arewacin Filistiya.
- Ibrahim ya kawo ɗan yankin mallaka daga Efron Bahitte domin ya bisne marigayiyar matarsa Sera a cikin kogo a can.
- Iyayen Isuwa sun damu a lokacin da Isuwa ya auro matan Hittiyawa guda biyu.
- Ɗaya daga cikin manyan jarumawan Dauda sunansa Yuriya Bahitte.
- Waɗansu daga cikin bãƙi da Suleman ya auro Hittiyawa ne. Waɗannan bãƙin mata suka karkatar da zuciyar Suleman daga Allah sabo da allohlin ƙarya da suka bautawa
- Har kusan kullum Hittiyawa sun kasance barazana ga Isra'ilawa, a zahirance da kuma a ruhaniyance.
(Hakanan duba: zuriya, Isuwa, bãƙo, Ham, maɗaukaki, Suleman, Uriya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 09:20-21
- Fitowa 03:7-8
- Farawa 23:11
- Farawa 25:10
- Yoshuwa 01:4-5
- Nehemiya 09:8
- Littafin Lissafi 13:27-29