607 B
607 B
Hamor
Gaskiya
Hamor mutumin Kan'ana ne da zama a birnin Shekem a lokacin da Yakubu da iyalinsa ke zama kusa da Sukkot. Shi mutumin Hibitiye ne.
- Yakubu ya sayi filin maƙabarta daga 'ya'yan Hamor.
- A lokacin da suke a can, ɗan Hamor mai suna Shekem ya yiwa ɗiyar Yakubu mai suna Dinatu fyaɗe.
- 'Yan'uwan Dinatu suka ɗauki fansa a kan iyalin Hamor suka kashe mazaje a birnin Shekem.
(Hakanan duba: Kan'ana, Hibitiye, Yakubu, Shekem, Sukkot)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 07:14-16
- Farawa 34:2
- Farawa 34:21
- Yoshuwa 24:32-33
- Littafin Alƙalai 09:28