948 B
948 B
Hamat, Hamitiyawa, Lebo Hamat
Gaskiya
Hamat wani birni ne mai muhimmanci a arewacin Siriya, arewa da ƙasar Kan'ana. Hamitiyawa zuriyar Nuhu ne ɗan Kan'ana.
- Wanan suna "Lebo Hamat" mai yiwuwa yana nufin dutse ne da ake wucewa ta kusa da shi a kusa da birnin Hamat.
- Waɗansu fassarori suna fassara "Lebo Hamat" da "mashigizuwa Hamat."
- Sarki Dauda ya yi nasara da sarkin maƙiyansa wato Sarki Tou na Hamat, hakan ya sa suka zama da zamantakewa mai kyau.
- Hamat na ɗaya daga ciki gidan ajiya na Suleman inda ake adana kayayyakin masarufi.
- Ƙasar Hamat ita ce inda aka kashe Sarki Zedekiya ta hanun Sarki Nebukadnezzar da kuma wurin da aka kame Sarki Yehoahaz ta hanun Sarkin Masar.
- Kalmar nan "Hamitiye" za'a iya fassara ta da "mutumin Hamat."
(Hakanan duba: Babila, Kan'ana, Nebukadnezzar, Siriya, Zedekiya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 18:3-4
- 2 Sama'ila 08:9
- Amos 06 :1-2
- Ezekiyel 47:15-17