715 B
715 B
Girkanci, Bagirke
Gaskiya
A kwanakin Sabon Alƙawari, Girka wani lardi ne na daular Roma.
- Kamar ƙasar da ake kira Girka a yau, tana can ne kusa da iyakokin Tekun Baharmaliya, da Tekun Aijiyan da Tekun loniya.
- Manzo Bulus ya yi ta biranen Girka ya kuma kafa majami'u a biranen Korint, Tassalonika da Filifiya mai yiwuwa da sauran waɗansu.
- Mutanen da suka zo daga Girka su ake kira Girkawa kuma harshen su shi ne "Girkanci". Hakanan mutane daga sauran lardunan Roma suma suna magana da harshen "Girkanci".
(Hakanan duba: Korint, Al'ummai, Girkawa, Ibraniyawa, Filifiya, Tassalonika)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Daniyel 08:21
- Daniyel 10:20-21
- Daniyel 11:1-2
- Zakariya 09:13