605 B
605 B
Goliyat
Gaskiya
Goliyat wani ƙaton soja ne a cikin sojojin Filistiyawa wanda Dauda ya kashe.
- Goliyat ya kai a ƙalla mita biyu zuwa uku na tsawo. Har kullum akan kira shi da gago sabo da shi ƙato ne sosai.
- Ko da yake Goliyat na da makaman da suka fi na Dauda sosai, Allah ya ba Dauda ƙarfi da ƙwarewa ya yi nasara da Goliyat.
- An aiyana Isra'ilawa akan sun yi nasara kan Filistiyawa a sakamakon nasarar Dauda bisa Goliyat.
(Hakanan duba: Dauda, Filistiyawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 20:4-5
- 1 Sama'ila 17:4-5
- 1 Sama'ila 21:8-9
- 1 Sama'ila 22: 9-10