673 B
673 B
Golgota
Gaskiya
"Golgota" sunan wani wuri ne inda aka gicciye Yesu. Sunansa ya zo ne daga kalmar Aremiyanci wadda ke nufin "Wurin Ƙoƙon Kai."
- Golgota tana bayan garun birnin Yerusalem, can kusa kusa. Tana nan ne gangaren Dutsen Zaitun.
- A waɗansu tsofaffin fassarori na juyin Littafi Mai Tsarki na turanci, an fassara Golgota da "Kalfari" wadda aka samo daga Latin wadda ke nufin "ƙoƙon kai."
- Juyi da yawa na Littafi Mai Tsarki na amfani da kalmar da ta yi kama da "Golgota" tun da yake an riga an baiyana kalmar a wurin.
(Hakanan duba: Aram, Tsaunin Zaitun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Yahaya 19: 17
- Markus 15:22
- Matiyu 27:33