ha_tw/bible/names/gilgal.md

943 B
Raw Permalink Blame History

Gilgal

Gaskiya

Gilgal sunan wani gari ne a arewacin Yeriko shi ne kuma wuri na farko da Isra'ilawa suka yi zango bayan sunƙetare Kogin Yodan domin shiga Kan'ana.

  • A Gilgal ne Yoshuwa ya jera duwatsu sha biyu waɗanda ya kwaso daga busasshen Kogin Yodan.
  • Gilgal shi ne birnin da Iliya da Elisha suka bari a lokacin da suka ƙetare Yodan a lokacin da za'a fyauce Iliya zuwa sama.
  • Akwai wurare da yawa da ake kira "Gilgal" a cikin Tsohon Alƙawari.
  • Kalmar nan "gilgal" ma'anarta ita ce "kewayen dutse" wato ana nufin wurin da aka kewaye da dutse aka gina bagadi.
  • A cikin Tsohon Alƙawari, wanan sunan har kullum yakan baiyana a matsayin "gilgal." Wanan zai iya nuna cewa ba wai wani wuri ne ba kawai, sai dai bayani ne game da wanirin wuri.

(Hakanan duba: Iliya, Elisha, Yeriko, Kogin Yodan)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 07:15-17
  • 2 Sarakuna 02:1-2
  • Hosiya 04:15
  • Littafin Alƙalai 02:1