670 B
670 B
Gileyad, Bagileye, Gilediyawa
Gaskiya
Gileyad sunan wani yanki ne mai duwatsu a gabashin Kogin Yodan inda kabilar Isra'ila na gidan Gad da Ruben da Manasse suka zauna.
- Wanan yankin shi ne kuma ake kira "ƙasa mai duwatsu ta Gileyad" ko "dutsen Gileyad."
- Haka nan Gileyad ya kasance sunaye na mutane da yawa a cikin Tsohon Alƙawari. Ɗaya daga cikinsu shi ne jikan Manasse. Wani Gileyad ɗin kuma shi nemahaifin Yefta.
(Hakanan duba: Gad, Yefta, Manasse, Ruben, kabilun Isra'ila goma sha biyu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 02:22
- 1 Sama'ila 11:1
- Amos 01:3
- Maimaitawar Shari'a 02:36-37
- Farawa 31:21
- Farawa 37:25-26