702 B
702 B
Galili, Bagalile, Galilawa
Gaskiya
Galili shi ne yanki mafi yawa a arewacin Isra'ila, yana kudu da Samariya. "Bagalile" shi ne mutumin da ke zama a Galili ko mazaunin Galili.
- Galili da Samariya da Yudiya su ne manyan lardunan Isra'ila a kwanakin Sabon Alƙawari.
- Galili tana iyaka da "Tekun Galili" daga gabas.
- Yesu ya yi rayuwa da kuma girma a garin Nazaret ta Galili.
- Mafi yawa daga cikin ayukan Yesu da koyarwarsa ya yi su ne a yankin Galili.
(Hakanan duba: Nazaret, Samariya, Tekun Galili)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 09:32
- Ayyukan Manzanni 13:31
- Yahaya 02:1-2
- Yahaya 04:3
- Luka 13:3
- Markus 03:7
- Matiyu 02:22-23
- Matiyu 03:13-15