771 B
771 B
Isuwa
Gaskiya
Isuwa ɗaya ne daga cikin tagwan 'ya'yan Ishaku da Rebeka. Shi ne aka fara haifa musu. Ɗan'uwansa shi ne Yakubu.
- Isuwa ya sayar da matsayinsa na ɗan fari ga Yakubu sabo da abinci.
- Tun da Isuwa shi ne na farko, ya kamata mahaifinsu Ishaku ya ba shi wata albarka ta musamman. Amma Yakubu ya yaudari Ishaku har ya ba shi albarka a memakon Isuwa. Da farko ya yi fushi har ya so kashe Yakubu, amma daga bisani ya gafarta masa.
- Isuwa yana da 'ya'ya da yawa da jikoki, waɗannan zuriya su ne suka zama babbar al'uma da ke zama a Kan'ana.
(Hakanan duba: Idom, Ishaku, Yakubu, Rebeka)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Farawa 25:26
- Farawa 25:29-30
- Farawa 26:34
- Farawa 27:11-12
- Farawa 32:5
- Ibraniyawa 12: 17
- Romawa 09:13