709 B
709 B
Ifraim, Ba'ifraime, Ifraimiyawa
Gaskiya
Ifraim shi ne ɗa biyu ga Yosef. Zuriyarsa ita ake kira Ifraimiyawa, suna ɗaya daga cikin kabilan Isra'ila sha biyu.
- Kabilar Ifraim na ɗaya daga cikin kabilu goma da ke arewacin Isra'ila.
- A waɗansu lokutan a cikin Littafi Mai Tsarki in an ambaci Ifraim ana magana ne akan ɗaukacin yankin arewacin Isra'ila.
- Yankin Ifraim yanki ne mai duwatsu ko tuddai, bisa ga bayanai akan ce da ita "ƙasa mai duwatsu ta Ifraim" ko "duwatsun Ifraim."
(Hakanan duba: mulkin Isra'ila, kabilun Isra;ila goma sha biyu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 06:66-69
- 2 Tarihi 13:4-5
- Ezekiyel 37:16
- Farawa 41:52
- Farawa 48:1-2
- Yahaya 11:54