912 B
912 B
Iliya
Gaskiya
Iliya ɗaya ne daga cikin mafiya muhimmaci a cikin annabawan Yahweh. Iliya ya yi anabci a kwanakin mulkin sarakunan Isra'ila da na Yahuda masu Yawa tare da sarki Ahab.
- Allah ya yi mu'ujuzai da yawa ta hannun ilya, wanda ya haɗa da tayar da yaron da ya mutu.
- Iliya ya tsautawa sarki Ahab sabo da bautar allolin ƙarya na Ba'al.
- Ya ƙalubalanci annabawan Ba'al zuwa gwaji wanda ya nuna Yahweh shi ne kaɗai Allah na gaskiya.
- A ƙarshen rayuwar Iliya Allah ya ɗauke shi sama tun yana raye ta wata hanya mai ban mamaki.
- Bayan ɗaruruwan shekaru Iliya tare da Musa sun baiyana tare da Yesu a kan dutse, sun kuma yi magana game da zuwan Yesu da shan wuyarsa da kuma mutuwarsa a Yerusalem.
(Hakanan duba: mu'ujuza, annabi, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 17:1
- 2 Sarakuna 1:3-4
- Yakubu 5:16-18
- Yahaya 01:19-21
- Yahaya 01:24-25
- Markus 09:5