902 B
902 B
Dauda
Gaskiya
Dauda shi ne sarki na biyu a Isra'ila ya kuma ƙaunaci Allah. Shi ne babban marubucin littafin Zabura.
- Tun Dauda na ƙaramin yaro yana kiwon tumakin iyalansu, Allah ya zaɓe shi ya zama sarkin Isra'ila na gaba.
- Dauda ya zama gwarzon mayaƙi ya kuma jagoranci Isra'ila zuwa yaƙi gãba da maƙiyansu. Ya yi nasara da Goliya hakan kuma sananne ne sosai.
- Sarki Saul ya so ya kashe shi, amma Allah ya kare shi, ya naɗa shi sarki bayan mutuwar Saul.
- Dauda ya yi wani zunubi mai ban takaici, amma ya tuba Allah kuma ya gafarta masa.
- Yesu Masihi, ana kiransa "Ɗan Dauda" domin shi zuriyar sarki Dauda ne.
(Hakanan duba: Goliyat, Filistiyawa, Saul (Tsohon Alƙawari))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sama'ila 17:12 -13
- 1 Sama'ila 20:34
- 2 Sama'ila 05: 02
- 2 Timoti 02:08
- Ayyukan Manzanni 02: 25
- Ayyukan Manzanni 13:22
- Luka 01:32
- Markus 02:26