1.1 KiB
1.1 KiB
Damaskus
Gaskiya
Damaskus shi ne babban birnin Siriya. Har yanzu yana nan a wurin da yake a cikin kwanakin Littafi mai tsarki.
- Damaskus na ɗaya daga cikin tsofafufin birane da har yanzu ake zama a cikin duniya
- A cikin kwanakin Ibrahim, Damaskus ita ce babbar cibiyar masarautar Aram(yanzu tana ƙasar da ake kira Siriya).
- A cikin dukkan Tsohon Alƙawari, akwai ayoyi da yawa da ke magana kan cunɗanya tsakanin mazaunan Damaskus da mutanen Isra;ila.
- Ananbce-anabce da yawa na littafi mai tsarki sun yi anabcin hallakarwar Damaskus. Ana tsammanin an cika wannan anabcin a lokacin da Asiriya ta hallakar da birnin a kwanakin tsohon Alƙawari, ko kuma ace akwai tsammanin kammala ƙarasa rushe wannan birni anan gãba.
- A cikin Sabon Alƙawari Saul Bafarisiye (wanda aka sani da suna Bulus) yana akan hanyarsa domin kamo masubi a birnin Damaskus a lokacin da yesu ya gamu da shi ya kuma sa shi ya zama mai bi.
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Tarihi 24:23-24
- Ayyukan Manzanni 09:1-2
- Ayyukan Manzanni 09: 03
- Ayyukan Manzanni 26:12
- Galatiyawa 01:15:-17
- Farawa 14:15-16