764 B
764 B
Saifros
Gaskiya
Saifros wani tsibiri ne cikin Tekun Baharmaliya, misalin kilomita 64 kudu da ƙasar Turki ta zamanin yau.
- Barnabas yana daga Saifros saboda haka mai yiwuwa ne ɗan'uwansa Yahaya Markus ma daga can yake.
- Bulus da Barnabas sun yi wa'azi tare a tsibirin Saifros a farkon tafiyar su ta bishara. Yahaya Markus ya bisu domin ya taimaka masu a wannan tafiyar.
- Bayan haka, Barnabas da Yahaya Markus suka sake ziyartar Saifros.
- A cikin Tsohon Alƙawari, an faɗi cewa Saifros na da arziƙin itatuwan rimi.
(Hakanan duba: Barnabas, Yahaya Markus, tekun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 04:36-37
- Ayyukan Manzanni 13:05
- Ayyukan Manzanni 15:41
- Ayyukan Manzanni 27:04
- Ezekiyel 27:6-7
- Ishaya 23:10-12