753 B
753 B
Kush
Gaskiya
Kush babban ɗan Ham ne wanda shi ma ɗa ne ga Nuhu. Shi kaka ne ga Lamirudu. 'Yan'uwansa biyu maza ana ce da su Masar da Kan'ana.
- A lokacin Tsohon Alƙawari, "Kush" sunan wani babban yanki ƙasa ne kudu da Isra'ila. Mai yiwuwa ne an ba ƙasan nan sunan ɗan Ham Kush.
- Tsohon yankin Kush ya maye ƙasa mai yawa da wataƙila a lokatai da dama ya haɗa har da ƙasashen zamanin yanzu kamar su Sudan, Masar, Itiyofiya, da ma wataƙila, Saudi Arabiya.
- Akwai wani mutum kuma da ake ce da shi Kush an faɗe shi a cikin Zabura. Shi kuma Ba'benyami ne.
(Hakanan duba: Arebiya, Kan'ana, Masar, Itiyofiya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 01:8-10
- Ezekiyel 29:10
- Farawa 02:13
- Farawa 10:6-7
- Irmiya 13:23