922 B
922 B
Karmel, Tsaunin Karmel
Gaskiya
Tsaunin Karmel yana cikin jerin wasu tsaunuka dake gaɓar Tekun Baharmaliya arewa da Filin Sharon. Ɗaya daga cikin tsaunukan mafi tsayi ya kai mita 546.
- Akwai kuma wani gari da ake kira "Karmel" yana cikin Yahuda, kudu da Tekun Gishiri.
- Wani mawadacin mai mallaƙar ƙasa Nabal da matarsa Abigel sun zauna kusa da garin Karmel inda Dauda da mutanensa suka taimaka a tsare masu sausayar tumakin Nabal.
- A bisa Tsaunin Karmel, Iliya ya ƙalubalanci annabawan Ba'al a wata gasa domin a tabbata cewa Yahweh ne kaɗai Allah na gaskiya.
- Domin ƙarin haske cewa wannan ba wai tsauni ɗaya ba ne, za a iya fassara "Tsaunin Karmel" haka, "tsaunin dake kan jerin tsaunukan Karmel" ko "jerin tsaunukan Karmel."
(Hakanan duba: Ba'al, Iliya, Yahuda, Tekun Gishiri)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 18:18-19
- 1 Sama'ila 15:12
- Irmiya 46:18
- Mika 07:14-15