1021 B
1021 B
Siseriya, Siseriya Filifai
Gaskiya
Siseriya birni ne mai mahimmanci a gaɓar Tekun Baharmaliya, kusan kilomita 39 kudu da Tsaunin Karmel. Siserriya Filifai birni ne dake arewa maso gabas da Isra'ila, kusa da Tsaunin Harmon.
- Waɗannan birane an raɗa masu suna haka saboda Sizozin da suka yi mulkin Roma.
- Siseriya ta gaɓar teku ta zama cibiyar birni ta lardin Roma na Yahudiya a lokacin da aka haifi Yesu,
- Manzo Bitrus ya fara wa al'ummai wa'azi a Siseriya ne.
- Bulus ya tashi daga Siseriya zuwa Tarsus a jirgin ruwa ya kuma wuce ta cikin birnin nan sau biyu a tafiyoyinsa na mai kai bishara.
- Yesu da almajiransa sun yi tafiya a kewayen lardin nan na Siseriya Filifai cikin Siriya. Dukka biranen biyu an sa masu sunan nan don tunawa da Herod Filib.
(Hakanan duba: siza, al'ummai, teku, Kamel, Tsaunin Hamon, Roma, Tarsus)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 09:30
- Ayyukan Manzanni 10:1-2
- Ayyukan Manzanni 25:01
- Ayyukan Manzanni 25:14
- Markus 08:27
- Matiyu 16:13-16