648 B
648 B
Betlehem, Ifrata
Gaskiya
Betlehem ƙanƙanen birni ne a cikin ƙasar Isra'ila, kusa da birnin Yerusalem. An kuma san shi da sunan nan "Ifrata" wanda watakila sunansa kenan tun farko.
- Ana kiran Betlehem "birnin Dauda" tunda yake a can aka haifi Sarki Dauda.
- Annabi Mika ya ce Almasihu zai zo daga "Betlehem Ifrata."
- Aka cika wannan anabci, sa'ad da aka haifi Yesu a Betlehem bayan shekaru da yawa.
- Ma'anar sunan nan Betlehem shi ne "gidan gurasa" ko "gidan abinci."
(Hakanan duba: Kaleb, Dauda, Mika)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Farawa 35:16
- Yahaya 07:42
- Matiyu 02:06
- Matiyu 02:16
- Rut 01:02
- Rut 01:21