610 B
610 B
Beriya
Gaskiya
A lokacin Sabon Alƙawari, Beriya (ko Berowa) birni ne mai wadata a kudu maso gabas da Makidoniya, kusan kilo mita 80 kudu da Tassalonika.
- Bulus da Silas sun gudu zuwa Beriya bayan abokansu Kiristoci sun taimake su suka kubce daga wasu Yahudawa waɗanda suka tada tarzoma a Tassalonika.
- Da mutanen Beriya suka ji Bulus yana wa'azi, suka bincike Nassi su tabbatar cewa abin da yake gaya masu gaskiya ne.
(Hakanan duba: Makidoniya, Bulus, Silas, Tassalonika)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 17:11
- Ayyukan Manzanni 17:13-15
- Ayyukan Manzanni 20:04